Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai yi wa al’ummar jihar Kano jawabi kan Coronavirus

Published

on

Da misalin karfe biyu na ranar yau Litinin ake sa ran cewa, gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai yi wa al’ummar jihar Kano jawabi kan bullar Annoba cutar Corona da aka samu a kasar nan da ma duniya baki daya.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano Abba Anwar ya shaidawa Freedom Radiyo cewa za’a yada wannan jawabi kai tsaye a gidan Radiyo da Talabijin mallakin gwamnatin jihar Kano da wasu daga cikin gidajen Radiyo masu zaman kansu a ciki da wajen jihar nan.

A ya yin jawabin ana sa ran gwamna Ganduje zai yi cikakken jawabi kan matakan da gwamnatin ke yi wajen tunkarar wannan cuta, idan an samu bullar ta a jihar Kano.

LABARAI MASU ALAKA

Covid-19: An fara rufe makarantun Islamiyya a Kano

Musulmai sun yi taron addu’a kan Coronavirus a Kano

Covid-19: Gwamnatin Kano ta bada umarnin rufe makarantun Allo dana Islamiyya

Haka kuma gwamnan zai yi bayani kan muhimmancin tsaftace jiki da wanke hannaye kamar yadda masana kiwon lafiya ke bayyanawa.

Yayin da kuma zai bukaci al’ummar jihar Kano da su baiwa kwamitin da aka kafa kan rigakafin cutar hadin kan da ya dace don kyautata lafiyar jama’ar jihar Kano bakidaya.

Kawo yanzu dai mutane 36 ne ake zargin sun kamu da cutar ta COVID- 19 a Najeriya yayin da mutum guda ya rasa ran sa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!