Coronavirus
Ganduje ya kaddamar da rabon “Face Mask” miliyan biyu ga Kanawa
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da fara rabon takunkumin rufe baki da hanci miliyan biyu ga al’ummar jihar.
A yayin kaddamar da rabon gwamna Ganduje yace matukar al’umma zasu rika bin dokokin kariyar Corona to babu shakka za a samu saukin yaduwarta a tsakanin al’umma.
Kazalika Gwamnan yace za ayi tsari wajen rabon ta yadda kowanne kwamishina akwai karamar hukumar da zai jagoranci rabawa.
Wakiliyar Freedom Radio ta fadar gwamnatin Kano ta rawaito mana cewa gwamna Ganduje yace sakamakon rashin tsafta a unguwanni da yanka dabbobi ke janyowa gwamnati ta amince a rika bude mayankar abbatuwa a duk ranakun Litinin da Alhamis da ake sassautar dokar kulle a jihar.
Karin labarai:
Covid-19: Sanya “Face Mask” ya zama dole a Kano
Ganduje ya rabawa likitoci kayan kare kai daga Corona
Har ila yau, Zahra’u Nasir ta rawaito mana cewa kafin kaddamar da fara rabon amawalin rufe baki da hancin, gwamna Ganduje ya kaddamar da asibitin mafitsara na Abubakar Imam a matsayin cibiyar masu killace Corona da gidauniyar Dangote ta gyara ta kuma samar masa da kayayyaki.
A ranar Lahadi ne dai gwamna Ganduje ya sanar da dokar tilasta sanya amawalin rufe baki da hanci ga al’umma a jihar.
You must be logged in to post a comment Login