Labarai
Ganduje ya musanta komawa makarantu ranar 14 ga watan Yuni
Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ake yadawa cewa ta amince a koma makarantu a ranar 14 ga waan da muke ciki.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Aliyu Yusuf a jiya Lahadi.
Sanarwar ta ce, labarin da ke yawo a shafukan sada zumunta kan komawa makaranta ba gaskiya bane.
Ganduje ya haramta amfani da injin Janareto a Kasuwar Sabon Gari
Ganduje zai dasa Bishiyu miliyan biyu domin kiyaye zaizayar kasa
Idan dai za a iya tunawa tun a watan Maris ne gwamnonin jahohin kasar nan suka dauki matakin rufe makarantu sakamakon barkewar annobar Covid-19 a kasar nan.
Sanarwar ta kuma bukaci iyaye da malaman makarantu da su kara hakuri, tana mai cewa tuni tattaunawa tayi nisa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jiha kan shirye-shiryen tsara yadda komawar dalibai makaranta zata kasance kan ka’idojin kula da lafiya.
You must be logged in to post a comment Login