Labarai
Ganduje ya musanta zargin dakatar da Murtala Sule Garo
Gwamnatin jihar kano ta ce wasikar da ke yawo a kafafen yada labarai cewa ta dakatar da kwamishinan Kananan hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo ba gaskiya bane.
Hakan na cikin wata sanarwa da mashawarincin gwamman na musamman ka Kafofin sada zumunta. Salihu Tanko Yakasai ya fitar.
Sanarwar ta kara dacewa wasikar dakatar da aikin ga kwamishinan dake yawo a kafafafen sada zumunta bata da tushi ballanta makama.
Ta cikin sanarwa Salihu Tanko Yakasai yace tuni jami’an yan sanda suka fara bincike domin nemo batagarin dake shirin tada zaune tsaye.
You must be logged in to post a comment Login