Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya yiwa jami’ar KUST na huce kan otel ɗin Daula

Published

on

Biyo bayan sake gabatar da ƙuduri akan haɗaka da gwamnati wajen sake mayar da hotal din Daula na zamani da wani kamfanin gine-gine ya sake gabatarwa a yau, gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci sakataren gwamnatin Kano da ya aike wa da jami’ar kimiyya da fasaha ta wudil cewa, an umarce su da su mayar da horarwar da suke yi zuwa cibiyar horarwa ta Aliko Dangote.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce sakataren ya sanar da su cewa gwamnati ta amince da mayar da hotal din Daula zuwa hotal na zamani mai ɗauke da shagunan zamani da kuma rukunin gidaje.

Ya kuma ce cibiyar horarwar ta Ɗangote zata zuba kayan aikin da suke bukata don gudanar da dukkan horarwar da suke yi a tsohon hotel din na Daula.

Kafin gabatar da ƙudurin a taron zauren majalisar zartarwar na Kano a yau Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taya ƴan Najeriya tare da shugaban ƙasa murnar takardar da aka miƙa wa shugaban ƙasa Muhammad Buhari ta nasara da Najeriya tayi wajen yaƙi da cutar Polio.

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce a nan Kano za a ci gaba da gudanar da allurar rigakafin Polio don cigaba da yaƙi da ita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!