Labarai
Ganduje zai dasa Bishiya miliyan 2 domin kiyaye zaizayar ƙasa
Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta gudanar da dashen bishiya guda miliyan 2 a sassan jihar Kano don kiyaye kwararowar hamada da barazanar zaizayar ƙasa.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, yayin bikin ranar muhalli ta duniya a bana.
Dakta Getso ya ce, “A yanzu haka ma’aikatar muhalli ta mayar da hankali wajen kula da dama-daman da ke jihar Kano tare da samar da hanyoyin da za a riƙa zubar da dagwalon masana’antu a yankunan chalawa da sharaɗa da kuma bompai ba tare da sun gurbata muhalli ba.
Ko kun san halin da Al’ummar Tofa suka shiga anan Kano
Majalisar dokokin jiha zata magance matsalolin muhalli
Ya ƙara da cewa”Da zarar an yi nasarar kawar da cutar corona, ma’aikatar muhalli za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaftar muhalli da take yi, don yaƙi da sauran cututtuka a jihar Kano”.
Kabiru Ibrahim Getso ya yi Kira ga jama’a da su riƙa tsaftace muhallan su, tare da gujewa ɗabi’ar sare bishiya ba tare da an mayar da madadin ta ba.
You must be logged in to post a comment Login