Labaran Kano
Ganduje : zamu samar da kayayyakin aiki don yakar cutar COVID-19
Gwamnatin jihar Kano tace zata tanadi dukkanin kayayyakin da jami’an kiwon lafiya zasuyi amfani dasu tare da kare Kansu daga kamuwa da cutar Corona.
Gwamna Ganduje ne ya bayyana hakan yau yayin taron majalisar zartarwa na yau da ya zo da wani sabon salo inda ba’a gudanar da shi a dakin taro na council chamber ba kamar yadda aka sab aba a Afrika Haouse
Kasancewar yana daga cikin matakan kaucewa cunkuso da kuma kamuwa da cutar Corona da gwamnatin Kano ta dauka kan kare kai daga COVID- 19
Gwamna Ganduje ya kara da cewa sun fito da tsari da dokoki na musamman domin a tabbatar da cewa al’umma sun yi don kaucewa bullar cutar a jihar Kano.
Ya kuma kara da shawartar mutane wajen bin dokoki da aka gundaya musu domin kare lafiyar su.
Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa a yayin taron majalisar zartarwar na Yau yan majalisar zartarwar yanayin zaman su akwai tazara sosai a tsakanin su.
You must be logged in to post a comment Login