Labaran Kano
Ganduje : zan yi duk mai yuwa wajen hana COVID-19 shigowa Kano
A yayin da kasashe a fadin duniya ke cike da fargabar kamuwa da cutar covid 19 Gwamnatin Kano ta ce zatayi duk mai yuwuwa wajen daukar matakan hana cutar shigowa jihar Kano.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan Yau lokacin da ya ke zagayawa wasu bangarori a filin saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano tare da jamian lafiya Jim kadan bayan daukar sa a filin jirgin saman daga Abuja.
Abdullahi Ganduje ya kara da cewa cutar ta Corona virus gaskiyace kasancewar an samu bullar ta a kasar a nan a don hakane ya zama wajibi daukar matakan kariya
Ya ce dukkanni wadanda suka shigo jihar nan daga ko ina ne tilas jamian lafiya sai sun auna su sun tabbatar basu dauke da cutar.
Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamna Ganduje ya kuma duba jirage guda biyu da suka sauka a Yau tare da duba yadda ake duba lafiyar wadanda suka sauka daga cikin jiragen.
You must be logged in to post a comment Login