Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje : zan yi duk mai yuwa wajen hana COVID-19 shigowa Kano

Published

on

A yayin da kasashe a fadin duniya ke cike da  fargabar kamuwa da cutar covid 19 Gwamnatin Kano ta ce zatayi duk mai yuwuwa wajen daukar matakan hana cutar shigowa jihar Kano.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan Yau lokacin da ya ke zagayawa wasu bangarori a filin saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano tare da jamian lafiya Jim kadan bayan daukar sa a filin jirgin saman daga Abuja.

Abdullahi Ganduje ya kara da cewa cutar ta Corona virus gaskiyace kasancewar an samu bullar ta a kasar a  nan a don hakane ya zama wajibi daukar matakan kariya

Ya ce dukkanni wadanda  suka shigo jihar nan daga ko ina ne tilas jamian lafiya sai sun  auna su sun tabbatar basu dauke da cutar.

Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamna Ganduje ya kuma duba jirage guda biyu da suka sauka a Yau tare da duba yadda ake duba lafiyar wadanda suka sauka daga cikin jiragen.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!