Connect with us

Labarai

Gianni Infantino na neman goyon bayan ƙasashen duniya

Published

on

Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, ya aike wa da dukkan ƙasashe 211 da ke tura tawagar ƙwallon ƙafa ƙarƙashin FIFA wasiƙa, inda ya yi musu tayin samun kuɗi har dala miliyan 40 ga duk ƙungiyar da ta goyi bayan shawararsa ta sayar da wani kaso na hannun jari na gasar cin kofin duniya da FIFA ke gudanarwa.

 

Gianni Infantino, ya bayyana cewa duk ƙungiyar da ta amince da wannan shiri kafin ranar 19 ga Satumba za ta karɓar kaso na farko na dala miliyan 20 daga ranar 1 ga Janairun 2027.

 

Haka kuma, ya ƙara da cewa, daga baya za a sake bai wa duk ƙungiyar da ta karɓi kason farko, kaso na biyu watau ƙarin dala miliyan 20.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!