Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta umarci ma’aikatan da aka yi wa aringizon albashi su mayar da kuɗin asusun ta

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci ma’aikatan da aka yi wa aringizon albashin watan Yulin 2026 su mayar da kuɗin zuwa asusun gwamnatin jihar domin gyara matsalar.

 

Gwamnatin , ta bayar da wannan umarni ne ta cikin sanarwar da Mataimakin Daraktan Kula da Tsarin Biyan Albashi na Sashen Asusun Gwamnatin Jihar Kano, Abdulhadi Hamza, ya fitar a ranar Talata 28 ga Yulin 2026.

 

Sanarwar ta ce bankin da abin ya shafa ya kasa dawo da kuɗaɗen da aka biya sau biyu zuwa asusun ma’aikatan, saboda haka aka buƙaci duk wanda ya karɓi aringizon kuɗin ya mayar da shi zuwa asusunta na bankin UBA

 

Ta kuma bayyana cewa, an kuma buƙaci ma’aikatan da abun ya shafa su miƙa shaidar biyan kuɗin zuwa Ofishin Babban Akanta na Jihar Kano da ke kan Titin Commissioner domin tantancewa da kuma ba su takardar shaidar dawo da kuɗin ga gwamnati.

 

Sanarwar ta kuma ce, Ofishin Babban Akanta ya buƙaci ma’aikatan da abin ya shafa su gaggauta bin umarnin domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da ingantaccen tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!