Labarai
Gidauniyar BAT da Ahlson sun baiwa manoma 400 tallafin a Kano
Manoman Masara 400, ne a jihar Kano suka samu Tallafin kayan Noma da suka haɗa da Taki da iri sai maganin ƙwari da Gidauniyar British American Tobacco tare da haɗin gwiwar kamfanin harkokin noma da Ahlson suka gudanar.
An kaddamar tare da bada taimakon a garin Ruwan Kanya dake ƙaramar hukumar Rano, da Garun Malam a garin Gafan da karamar hukumar Kura.
Da yake jawabi a harshen Turanci,shugaban gidauniyar kamfanin British American Tobacco na ƙasar nan Adetola Oniyolu ,wanda shugaban kamfanin Ahlson Ali Ahmad Ali , yayi bayani da Hausa a madadin sa , yace sun zaɓo Manoman ne tare da basu Tallafin don inganta noma da samar da abinci mai gina jikin ɗan Adam.
Wasu daga cikin Manoman da suka samu Tallafin sun bayyana cewa ‘ire-iren tallafin ne cigabane da zai kawo bunkasar noma a Jihar dama kasar Baki daya’.
Zagayen bada Tallafin zai cigaba da gudana a ƙananan hukumomin Gwarzo, Kumbotso sai Dawakin Kudu da Kabo da Rimin Gado , inda ake gudanar dashi tare da haɗin gwiwar kungiyoyi da hukumomin Noma da suka haɗar da GIZ sai Harvest Plus da hukumar KNARDA da ma’aikatar Gona ta jiha da ta Tarayya.
Rahoton: Aminu Halilu Tudun Wada
You must be logged in to post a comment Login