Manyan Labarai
Gobara ta hallaka ƙananan yara ƴan makaranta 20 a Nijar
A ƙalla ƙananan yara ɗalibai ashirin ne suka ƙone ƙurmus, a wata gobara da ta tashi a wata makaranta da ke babban birinin Yamai na jamhuriyar Nijar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gobarar ta tashi ne da yammacin jiya Talata, a makarantar Kongolba da ke Unguwar Ɗanladi a Yamai.
Wakilin Freedom Radio a Yamai Ishu Mamman ya ce, an gina makarantar nw da zana, wanda hakan ya sanya wutar ta riƙa ci babu ƙaƙƙautawa, kafin daga bisani jami’an kashe gobara su kawo ɗauki.
Ya ci gaba da cewa, dukkan kujerun zaman ɗalibai da kayyakin makarantar sun ƙone ƙurmus, kuma tuni al’umma suka shiga jimami kan lamarin.
Sai dai har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto hukuma a ƙasar ba ta ce komai ba a kai.
Hotunan yadda lamarin ya faru.
You must be logged in to post a comment Login