Connect with us

Labarai

Gobara ta lakume kasuwar Takumbo da wasu gine-gine a Kano

Published

on

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce gobara mai tsanani ta tashi a daren ranar 11 ga Yuni, 2026, a kan titin Murtala Mohammed Way kusa da bankin FCMB a karamar hukumar Fagge.

 

A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar, an samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:54 na dare daga wani jami’in hukumar, HFS Ibrahim Sabo, inda aka sanar da aukuwar gobarar. Nan take aka tura jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar da sauran tashoshin cikin birnin Kano zuwa wurin.

 

Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga kasuwar Takumbo (salvage yard), inda ta lalata kayayyaki masu yawa kafin daga bisani ta bazu zuwa bene na sama na ginin Kanawa Building, tare da lalata ofisoshi biyu, falo biyu, bandakuna biyu da kuma kicin guda. Haka kuma, ta shafi shaguna biyu da ke kasa na kamfanin TUSRAYS NIG. LTD. Hukumar ta bayyana cewa walƙiyar lantarki ce ta haddasa gobarar, tare da yin kira ga jama’a su dauki matakan kariya da kuma gaggauta kai rahoton duk wata gobara zuwa tashar kashe gobara mafi kusa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!