Jigawa
Gobe Jigawa zata cika shekaru 29 da kafuwa
Gwamnatin jihar Jigawa ta tsayar da gobe Alhamis a matsayin ranar hutu a jihar don Murnar cikar jihar shekaru 29 da kafuwa.
Hakan na cikin sanarwar da shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Hussaini Ali Kila ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da ranar wajen gudanar da addu’o’i na musamman ga jihar da ma kasa baki ɗaya don samun ɗauki daga wajen Ubangiji na ci gaba da samar da ayyukan bunƙasa jihar.
Ta cikin sanarwar, gwamnan jihar Alhaji Badaru Abubakar ya miƙa sakon ta’aziyyar sa ga ɗaukacin al’ummar jihar bisa rasuwar tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Birgediya Janar Olayinka Sule mai ritaya wanda ya rasu a ranar 23 ga watan da muke ciki yana da shekara 72.
Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana rasuwar tsohon gwamnan da cewa ɗaya ne daga cikin waɗanda suka taka rawa wajen tabbatar da ganin an ƙirƙiro jihar ta Jigawa.
You must be logged in to post a comment Login