Labarai
Gobe laraba ta zamo ranar tunawa da yin katin shidar ‘yan kasa – Pantami
Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba sha shida ga watan Satumba a matsayin ranar yin katin shidar ‘yan kasa da nufin tallafawa ‘yan Najeriya su mallaki katin zama dan kasa a Najeriya.
Ministan sadarwar zamani Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da mai magana da yawun ministan Mrs Uwa Sulaiman ta fitar a yau Talata.
Ta cikin sanarwar Dakta Isah Fantami ya jaddadawa ‘yan kasar nan mahimmancin mallakar katin dan kasa inda ya ce, za su ci gaba da kyautata hanyoyin samar da katin ga kowanne dan kasa.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a gudanar da bikin bana ne ta kafar Internet, yana mai cewa, katin zama dan kasa na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki kasa da kuma kariya ga yan kasa a duk inda suka tsincisu kansu.
You must be logged in to post a comment Login