Kiwon Lafiya
Gwamantin tarayya ta yi gargadi kan cin Ganda
Ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayyar Nijeriya, ta shawarci al’umma da su daina cin Ganda da kuma dabbobin daji saboda suna da matukar hadari wajen janyo kamuwa da cutuka.
Hakan dai na zuwa ne bayan da ma’aikatar ta sanar da bullar cutar Anthrax a wasu kasashen nahiyar yammacin Afirka.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar, Dakta Ernest Afolabi Umakhihe da ya fitar yau Litinin.
Sanarwar ta ce, an fara samun bullar cutar ne a Arewacin kasar Ghana wadda ke da iyaka da kasashen Burkina Faso da Togo, lamarin da ya jefa yankin cikin hadari sakamakon bullar wannan annoba.
Haka kuma, sanarwar, ta bayyana cewa, “Cutar da yi sanadin lakume rayukan dabbobi da dama kasancewar tana shafar dabbobi da mutum.
“Ta cikin sanarwar dai, ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, ana samun cutar ta Anthrax spores ne a wasu halittu a cikin ƙasa, kuma galibi ta na shafar dabbobin gida ne da kuma na daji.”
“Mutane na iya kamuwa da cutar ta Anthrax idan suka yi mu’amala da dabbobin da suka kamu da cutar ko kuma gurbatattun kayayyakin dabbobi kamar fatu da sauransu. Duk da haka, Anthrax ba cuta ce mai yaduwa ba don haka, ba za a iya kamuwa da ita ta hanyar kusanci da mai cutar ba,” A cewar sanarwar.
“Alamomin cutar anthrax kamar Mura ce sun hada da Tari da Zazzabi da Ciwon Jiki, kuma idan ba a gano cutar ba kuma a yi maganinsu da wuri, suna haifar da Ciwon Huhu mai tsananin Wahalar numfashi sai cutar firgita da kuma mutuwa.”
Haka kuma, Sanarwar ta gargadi jama’a game da kusanci da dabbobin da ba a yi musu allurar cutar Anthrax ba, domin ana iya kamuwa da ita ga mutum cikin sauki ta hanyar shakar kwayar cutar da ko amfani da Fata ko Nama har ma da Madarar dabbobin da ke dauke da cutar.
You must be logged in to post a comment Login