Labarai
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin gano musabbabin mutuwar ɗalibar St. Louis

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin mutuwar ɗalibar makarantar sakandere ta St. Louis da ke jihar.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na jihar kano ,Dakta Gwani Ali Haruna Makoda, zai gudanar da cikakken bincike kan yadda lamarin ya faru.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce kwamitin zai kuma binciki zarge-zargen cin zarafi, gallazawa ko hukunci ba bisa ƙa’ida ba da ake zargin wasu ɗalibai sun yi, tare da daukar matakan hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Ana sa ran kwamitin zai miƙa rahotonsa ga gwamnati cikin wa’adin da aka tsara.
You must be logged in to post a comment Login