Labarai
NESREA ta fara bincike kan zargin zubewar sinadari mai hatsari a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Tarayya, NESREA, ta fara gudanar da bincike kan wani zargin zubewar sinadari mai haɗari da ya faru a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan da wata babbar mota ta yi hatsari tare da barin wani farin kumfa a wurin da lamarin ya auku.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce jami’anta na reshen jihar Kaduna sun ziyarci wurin domin tattara bayanai tare da ɗaukar samfurin farin kumfar, ƙasa da kuma ruwan wani rafin da ke kusa domin gudanar da gwajin kimiyya kan ainihin sinadarin da kuma tasirinsa ga muhalli.
Rahotannin farko sun nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan wata babbar mota ta zubar da kayan da take ɗauke da su, lamarin da ya jawo hankalin jama’a da dama da suka riƙa tsayawa suna ɗaukar hotuna da bidiyo na abin da suka gani.
You must be logged in to post a comment Login