Connect with us

Labarai

Hon. Abba Anas Adamu ya rasu a hannun ‘yan bindigan da suka sace shi

Published

on

Tsohon ɗan majalisar wakilai na Tarayya Hon. Abba Anas Adamu, ya rasu a hannun ‘yanbindiga bayan sace shi da suka yi kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

 

Rahotanni sun bayyana cewa a makon da ya gabata ne masu garkuwa da mutane suka sace wasu manyan ‘yan siyasa daga Jihar Jigawa, ciki har da Abba Anas Adamu, wanda ya taɓa wakiltar mazabar Birniwa/Guri/Kiri Kasama a Majalisar Tarayya kuma ya taɓa shugabantar Karamar Hukumar Guri, tare da Ali Tukur Gantsa, tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar kuma jigo a Jam’iyyar ADC a jihar, yayin da suke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

 

Sanata Sabo Mohammed Nakudu CON daga Jihar Jigawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana ta’aziyyarsa a shafinsa na Facebook.

 

Rahotonni sun tabbatar cewa Hon. Abba Anas Adamu ya rasu a hannun masu garkuwar, Za’a gundanar da Jana’izar Marigayi Hon. Abba Anas Adamu a yau Talata, a gidansa da ke Zangon Dakata bayan Ofishin hukumar WAEC da ke kan Titin Dakata zuwa Bela, da Karfe 10:00 na safe.

 

Yayin da kuma aka samu labarin kubutar Ali Tukur Gantsa daga hannun masu garkuwar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!