Labarai
Mutum daya ya mutu tare da jikkatar wasu sakamakon rushewar gini a Kano

Wani gini mai hawa biyu ya rushe a safiyar yau Juma’a a kan titin Sultan Road da ke unguwar Nassarawa GRA a birnin Kano, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da ceto wasu tsakanin mutum huɗu zuwa biyar a ƙarƙashin baraguzan ginin.
Rahotanni daga wajen da abin ya faru sun nuna cewa jami’an agaji da masu aikin ceto sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto da kuma tantance girman asarar da aka yi. Wani ganau ya shaida cewa ana zargin rashin ingancin kayayyakin da ake amfani da su wajen ginin na iya kasancewa cikin abubuwan da suka haddasa rushewar ginin, sai dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.
Freedom Radio ta ziyarci wurin da lamarin ya faru domin tattara bayanai daga shaidu da hukumomin da abin ya shafa. Ku kasance tare da mu domin jin cikakken rahoto a cikin labaranmu na gaba.
You must be logged in to post a comment Login