Labarai
Gwamna Mai Mala ya ɗage haramcin amfani da babura a wasu ƙananan hukumomi
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya sanar da ɗage haramcin amfani da babura a ƙananan hukumomin jihar guda bakwai.
gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam ya fitar jiya Litinin a Damaturu babban birnin jihar.
Sanarwar ta ce, za a iya yin amfani da babura daga karfe shida na safe zuwa shida na yamma a kowace rana.
Tun a shekarar 2012 ne dai gwamnatin lokacin ta Ibrahim Gaidam, ta sanya haramci kan amfani da babura a faɗin jihar da nufin dakile yunkurin amfani da su wajen aikata ta’addanci musamman lokacin da hare-haren Boko Haram suka yi kamari a jihar.
Sai dai gwamna Mai Mala Buni ya ɗage haramcin a kan wasu ƙananan hukumomi goma cikin goma sha bakwai na jihar a watan Janairun bara.
You must be logged in to post a comment Login