Labarai
Yaki da ‘yan bindiga: Gwamna Masari ya tura Karnuka gadin makarantun kwana a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta amince da fara amfani da karnuka don kula da makarantun kwana da ke fadin jihar baki daya.
Kwamishinan ilimi na jihar Dr. Badamasi Chiranchi ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a garin Katsina.
Ya ce, karnukan za su rika tallafawa jami’an tsaro da ke kula da tsaron makarantun kwana ne da ke jihar.
A cewar kwamishinan an bai wa gwamnatin jihar shawara ce kan daukar wannan mataki, saboda karnuka suna da nasibi da Allah ya yi musu da za su iya gano marar gaskiya tun daga nesa.
A watannin baya ne dai wasu ‘yan bindiga suka sace daliban makarantar sakandiren Kankara su 342 kafin daga bisani jami’an tsaro su samu nasarar ceto su.
You must be logged in to post a comment Login