Labarai
Gwamna Radda ya amince da kashe Biliyan 4 don aiwatar da kashi na 2 na ayyukan unguwanni

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da ware Naira biliyan 4 domin aiwatar da kashi na 2 na shirin ayyukan ci gaban al’umma a dukkan unguwanni 361 na jihar.
wannan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar Laraba 5 ga Agustan 2026.
Ya ce, kowace unguwa za ta karɓi Naira miliyan 10 domin aiwatar da ayyukan da al’ummar yankin suka zaɓa bisa ga buƙatunsu.
Sanarwar ta ce, amincewar ta biyo bayan nasarorin da aka samu a kashi na farko na shirin, domin ci gaba da bunƙasa ayyukan ci gaba a matakin al’umma.
Haka kuma majalisar ta amince da fitar da rahoton ci gaban Shirin Inganta Yanayin Kasuwanci na BERAP na shekarar 2025, tare da sayo sinadaran tace ruwa da kuma samar da motocin dakon ruwa domin ci gaba da samar da tsaftataccen ruwa ga mazauna birnin Katsina yayin gyaran cibiyar samar da ruwa.
You must be logged in to post a comment Login