Labarai
Gwamna Radda ya amince da nada shugaban hukumar yaki da Rashawa
Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya amince da nadin sabon shugaban hukumar yaki da rashawa da kuma shugaban hukumar kula da al’amurorin kananan hukumomin jihar.
Ta cikin sanarwar da sakataren yada rabaran gwamnan jihar Malam Ibrahim Kaula, ya fitar, ya ce nadin ya biyo bayan samar da hukumar da gwamna Radda yayi a baya bayan nan.
Sabbin wadanda aka nada sun hadar da Mai shari’a Lawal Garba mai ritaya a matsayin shugaban hukumar ta Anti-Corruption, da Alhaji Usman Mamman-Maska a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin kananan hukumomin jihar.
You must be logged in to post a comment Login