Connect with us

Labarai

Ni da Atiku Abubakar a shirye muke domin janye takarar mu – Rotimi Amaechi

Published

on

Tsohon gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake ya janye daga takarar sa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, idan farashin litar fetur ya koma naira 600.

 

Amaechi ya bayyana hakan ne yayin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana shakku kan ikirarin shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa Najeriya ta shiga wani sabon zamanin wadata.

 

Ya ce idan aka tabbatar masa da cewa ana sayar da litar fetur kan naira 600 a gidajen mai, zai janye takarar sa tare da Atiku Abubakar, sannan ya koma goyon bayan shugaba Tinubu a babban zaben 2027.

 

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar ADC ya kuma kalubalanci duk wanda ke shakkar maganarsa da ya raka shi da kyamara zuwa gidan mai, domin tabbatar da farashin da ake sayar da fetur.

 

Kalaman Amaechi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan tsadar man fetur, hauhawar farashin kayayyaki da kuma halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!