Connect with us

Labarai

Gwamna Zulum ya nemi shugaba Buhari ya gayyato sojojin Chadi don yaki da BH

Published

on

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyato sojojin kasar Chadi, don su taimaka a yakin da ake yi da mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya har karo uku, wanda ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai wa kwambar motocin sa harin kwanton bauna.

A cewar gwamna Baba Gana wannan dai na nuna irin yadda ayyukan ta’addanci ke kara tsananta a yankin arewa maso gabashin kasar nan, wanda kuma ya zama wajibi a kara zage dantse wajen dakile ayyukan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!