Labarai
Yan wasa da masu horaswa 11 sun mutu a hatsarin jirgin Faransa

Wani jirgin sama ɗauke da ƴan wasan zamiya ya yi hatsari a Gabashin Faransa kuma dukkan mutane 11 da ke ciki sun rasu.
Mutanen sun haɗa da masu horaswa biyar da ɗalibansu biyar da kuma matuƙin jirgin.
Jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗa bayan ya tashi, kuma wasu daga cikin ƴan uwan mutanen da ke ciki suna kallo lokacin da ya faɗo.
Jirgin ya faɗo ne kusa da wata unguwa, kuma babu wanda abun ya shafa.
Kawo yanzu babu tabbacin abin da ya jnyo hatsarin.
You must be logged in to post a comment Login