Connect with us

Labarai

Najeriya ta tura sojoji zuwa Gambia domin wanzar da zaman lafiya

Published

on

‎‎Rundunar Sojin Sama ta kasar nan ta sanar da tura sabbin sojoji 198 zuwa ƙasar Gambia domin ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya ƙarƙashin tawagar ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS.

 

‎‎A cewar rundunar, an yi jigilar sojojin ne ta jirgin dakon kaya na C-130H, inda aka kai dakarun rundunar domin su maye gurbin waɗanda ke cikin rundunar NIGCOY 10 ECOMIG, bayan sun kammala wa’adin aikinsu.

‎Rundunar ta bayyana cewa an gudanar da sauya dakarun ne a zagaye biyu tsakanin 26 da 30 ga Mayun 2026, tare da jigilar kayan aikin soji da kayayyakin amfanin mutanen da aka tura domin tabbatar da cewa an mika ragamar aikin cikin tsari ba tare da tangarɗa ba.

‎NAF ta ce nasarar gudanar da wannan aiki ta nuna irin ƙarfin da rundunar ke da shi wajen jigilar dakaru cikin gaggawa zuwa ƙasashen waje domin tallafa wa ayyukan wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!