ilimi
Gwamnati Kano ta bada umarnin a bude makarantu ranar Litinin don fara karatun zango na biyu
- Gwamnatin Jihar Kano ta bada Umarnin a bude makarantun Firamare, Dana sakandire farkon mako Mai kamawa, don fara karatun zango na biyu.
- Daliban da suke makarantun jeka ka dawo zasu koma makarantun su ne a ranar Lahadi 8 ga watan Junairu.
- Daliban da suke makarantun jeka ka dawo Kuma, zasu koma ranar Litinin 9 ga watan Junairu don fara karatun zango na biyu.
- Duk dalibin da bai koma makaranta ranar da gwamnati ta bukaci a koma ba, akwai hukuncin da aka tanadar masa.
Gwamnatin Jihar Kano ta bada Umarnin a bude makarantu firamari, dana sakandire farkon mako Mai kamawa, don fara karatun zango na biyu.
Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan ilimi na Jihar Kano Ya’u Abdullahi ‘Dan Shana, ta fito ne ta hannun Mai magana da yawun ma’aikatar Aliyu Yusuf a ranar asabar 7 ga watan Junairu.
Kwamishinan ya ce ‘daliban da suke makarantun kwana a fadin Jihar nan zasu koma makarantun su ne a ranar Lahadi 8 ga watan Junairu don shirye-shiryen fara karatun zango na biyu’.
‘Yayin da daliban da suke makarantun jeka ka dawo Kuma zasu koma Makarantar ranar Litinin 9 ga watan Junairun’.
Ya’u Abdullahi ‘Dan Shana ya jinjinawa ma’aikatansa dangane da irin goyon bayan da suke bashi wajen kawo cigaban ilimi, tare da mika godiyarsa ga iyayen yara.
‘Dan Shana ya Kuma yi Kira ga iyayen yara dasu cigaba da basu goyon baya, ta hanyar bin dokokin da aka tsara a makarantun’, don samar da cigaba a fannin ilimi.
Yana mai cewa ‘akwai hukuncin ga duk Wani dalibi da bai koma makaranta ba a ranar da gwamnati ta bada Umarnin a koma’.
Tag.Ma’akatar ilimi ta Jihar Kano. Ya’u Abdullahi ‘Dan Shana. Aliyu Yusuf. Freedom Radio. Shamsiyya Farouk Bello.
You must be logged in to post a comment Login