Connect with us

Labarai

Atiku ya mayar wa Shugaba Tinubu martani kan sukar shirin dawo da tallafin man fetur

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar wa Shugaba Bola Tinubu martani kan sukar da ya yi masa game da shirin dawo da tallafin man fetur.

Tinubu ya ce shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027 ya nuna rashin fahimtar tattalin arziki da yadda ake tafiyar da gwamnati.

Sai dai Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙara jefa ‘yan kasar nan cikin tsadar rayuwa, inda yace cire tallafin ya haifar da tashin farashin man fetur da sufuri da na kayan abinci.

Ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta cire tallafin ne ba tare da samar da isassun matakan rage radadin tsadar rayuwa ga ‘yan kasar nan ba.

A nasa bangaren, shugaba Tinubu ya ce cire tallafin ya taimaka wajen ƙara kuɗaɗen da gwamnatocin jihohi ke samu, wanda ya ba su damar biyan albashi da gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!