Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Gwamnati za ta binciki yawaitar mace-macen da ake samu a Kano

Published

on

Al’ummar kwaryar birnin Kano sun shiga cikin zullumi sakamakon yawaitar mace-mace da ake samu a yankin kwaryar birnin.

Rahotonni na nuni da cewa an samu karuwar adadin wadanda ke rasuwa a birnin Kano kuma mafi yawa mutuwar tafi shafar dattijai.

Wani mai aikin hakar kabari a makabarta da Freedom Radio ta zanta da shi ya ce yayi matukar kaduwa bayan da ya ga adadin wadanda ake kawo sun ninninka na baya.

Wannan batu ya sanya hatta masu amfani da kafafan sada zumunta na zamani suna ta cin karo da labarin rasuwa a kafafan.

Ku kalli wadansu sanarwar mutuwa da aka wallafa a shafin Facebook a Kano.











Har ila yau, ana ta yada wasu alkaluma da ba a tantace ba wadanda suke nuna adadin wadanda suka rasu a wannan yanayin.

Sai dai manazarta na ganin cewa zai yi wuya a iya tantance adadin wadanda suka rasu a Kano cikin sauki, kasancewa bisa al’ada masu aiki a makabarta basa tattara bayanan mamatan da ake binnewa a makabartu.

Sai dai cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta fitar da tsakar ranar litinin ta ce ta samu labarin mace-macen da ake wallafawa a kafafan na sada zumunta.

Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’ar hurda da jama’a ta hukumar Hadiza Namadi ta ce kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa tuni su ka fara bincike kan wannan al’amari domin tabbatar da hakikanin abinda ke faruwa.

Hari la yau Dakta Tsanyawa ya ce da zarar sun kammala bincike zasu sanar da al’umma halin da ake ciki.

A karshe kwamishinan yayi addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka rasu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!