Labarai
Gwamnatin Adamawa ta dakatar da Sakataren hukumar kula da makarantun Sakandare

Gwamnatin jihar Adamawa ta dakatar da sakataren zartarwar hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta jihar, Mista Birsan Penuel, bisa zargin wasu kura-kurai wajen gudanar da ayyukansa.
Babban Sakataren yada Labaran Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, Humwashi Wonosikou, ne ya bayyana hakan a Yola babban birnin jihar.
Ya kuma ce an dakatar da jami’in ne domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Haka kuma, ya ce, an umarci babban sakataren hukumar da ya jagoranci ayyukanta, domin tabbatar da cewa ba a samu tsaiko a harkokin hukumar ba.
You must be logged in to post a comment Login