Labarai
Hukumar NSCDC ta gargadi masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba

Hukumar tsaro ta Civil Defence, ta gargadi masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa rashin sanin doka ba zai zama hujjar kubuta daga hukunci ba.
Kwamandan hukumar da ke sanya ido kan harkar ma’adinai, Attah Onoja, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Ya ce rundunar ta ƙara tsaurara matakan sintiri da tabbatar da bin dokokin hakar ma’adinai a faɗin ƙasar.
Ya ce matakan na da nufin dakile hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, kare masu zuba jari masu bin doka da inganta kudaden shiga na gwamnati. Ya kuma ce jami’an za su ci gaba da gudanar da ayyukan tabbatar da bin doka a faɗin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login