Labarai
Gyare-gyaren da ake yi a bangaren harkokin ruwa sun fara haifar da sakamako mai kyau- NPA

Gwamnatin Tarayya ta ce gyare-gyaren da take yi a bangaren harkokin ruwa sun fara haifar da sakamako mai kyau
A cewar ta kayayyakin da ake sarrafawa a tashoshin jiragen ruwa ya karu da kashi 12 da digo 3 cikin dari.
Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, NPA, ta bayyana hakan a rahotonta na ayyukan zangon watanni uku na biyu na shekarar 2026.
Rahoton ya nuna cewa an sarrafa sama da tan miliyan 35 da dubu 700 na kayayyaki a tashoshin jiragen ruwan kasar nan, idan aka kwatanta da tan miliyan 31 da dubu 800 a makamancin lokacin a bara.
Haka kuma, yawan manyan jiragen ruwa da suka kammala ayyukansu ya karu da kashi 14 da digo 4 cikin dari, yayin da zirga-zirgar kwantena ta karu da kashi 11 da digo 3 cikin dari, inda aka samu sama da kwantena dubu 602.
Hukumar ta ce safarar motocin da aka shigo da su ta tashoshin ruwa ma ta karu da kashi 18 da digo 3 cikin dari.
A bangaren fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kuma, an samu karin kashi 22 cikin dari, abin da hukumar ta ce na nuna ingantuwar harkokin fitar da kayayyaki daga Najeriya.
Manajan Daraktan hukumar ta NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya ce hukumar za ta mayar da hankali wajen zamanantar da tashoshin jiragen ruwa, da amfani da fasahar zamani da inganta tsaro da ayyukan tashoshin.
Ya ce ana kuma kokarin bunkasa tashoshin Lekki da Badagry da sauran tashoshin gabashin kasar nan, domin rage cunkoso a tashoshin Lagos da kuma saukaka harkokin kasuwanci.
You must be logged in to post a comment Login