Kiwon Lafiya
Gwamnatin Benue ya ce zai marawa gwamnatin tarayya dakile tashe-tashen hankula a yankinsa
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yace zai bayar da goyon baya ga duk wani yunkurin da gwamnatin tarayya zatayi da suka hadar da tura jami’an soji jihar sa, matsawar hakan zai taimaka wajen dakile tashe-tashen hankulan.
Sai dai yace ba zai goyi bayan shirin gwamnatin tarayya ba, na kafa wani yankin na daban ga makiyaya, har sai gwamnatin tayi masa bayanin da zai gamsu da shi kan hakan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan ganawar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan rikicn da ya kunno kai jihar sa,wanda ya janyo asarar rayuka da dama.
Ya ce tun da farko ya gana da shugaba Buhari ta wayar tarho kan batun rikicin, sai dai kuma daga bisani ne ya nemi ganawa ta musamman da shugaba Buhari, boyi bayan samun nasarar tsayar da rikicin a halin yanzu.
Ko da aka tambaye shi kan matsayar sa game da batun mika bukatar tura dakarun soji jihar sa, sai yace duk wani yunkurin da zai dakile kashe-kashen da ak yiwa al’ummar jihar sa, zai bayar da goyon bayan da ya dace ba tare da bata lokaci ba