Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Borno ta ce ta dauki matakin rusa unguwar Galadima
Gwamnatin Jihar Borno ta ce ta dauki matakin rusa unguwar Galadima sakamakon kaurin sunan da unguwar ta yi wajen shan miyagun kwayoyi.
Mai taimaka na musamamn ga gwamnan jihar kan harkokin yada labarai, Mallam Usman Maji Dadi Kumo shi ne ya sanr da hakan ga manema labarai inda ya ce unguwar ta yi kaurin suna wajen shan kwaya, da tabar wiwi, da kodin da duk wani abin da ke sanya maye.
Ya kuma kara da cewa shaye-shayen da ake yi a unguwar sun munana, kuma gwamnati ba za ta bar duk wani abu da ke da hadarin sake kawo tashin hankali a jihar ba.
A cewarsa, wutar da ta kone jihar, ba za a bari ta sake kamawa ba.
A saboda haka ya ce za a rushe ilahirin unguwar bayan an biya dukkanin wadanda suka mallaki filaye bisa ka’ida a unguwar diyya.
To sai dai kuma wasu na fargabar wannan mataki na gwamnatin Borno ya yi tsauri musamman bisa la’akari da yadda jihar ke fama da matsalar ‘yan gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram.