ilimi
Gwamnatin Kaduna ta mayar da Malaman firamare fiye da 1,000 da ta sallama bakin aiki
Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da mayar da malaman makarantar firamare 1244 da ta sallama bakin aiki.
Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna Hajiya Hauwa Muhammad ce ta bayyana hakan, cikin sanarwar da aka fitar a jiya Laraba.
Hajiya Hauwa ta ce malamai 1,266 ne aka yi wa jarrabawar gwajin cancantar, yayin da 22 a cikinsu aka tsame su daga jadawalin albashin gwamnati.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa a Yunin 2022 ne, ma’aikatar ilimin ta kori malaman Firamare 2,357 saboda gaza tsallake jarrabawar.
You must be logged in to post a comment Login