Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kaduna ta bullo da binciken gida-gida don kare al’umma daga kamuwa da cutuka masu yaduwa
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bullo da wani tsari na gudanar binciken gida-gida domin kare al’ummarta daga kamuwa daga cutuka masu yaduwa a Jihar da ma makwabtanta.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta Paul Dogo ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya a Kaduna, a kokarin kare yaduwar cutuka irin su Kwalara da Sankarau da Kyanda da makamantansu.
Dokta Paul Dogo ya ce ya zuwa yanzu ba su samu labarin bullar ko wace irin cuta ba a cikin kananan hukumomi 23 na Jihar, sannan ya bada tabbacin kare aukuwar barkewar cututtuka a Jihar.
Kamishinan ya tabbatar da cewa sun tanadi magunguna domin rarrabawa Asibitoci da zarar an samu bullar wata cuta a Jihar ciki har da maganin Tarin fuka.
Har ila yau, ya kar da cewa tun daga watan Nuwamban shekarar 2012 ba samu bullar cutar Polio a Jihar ba, a don haka ma suka ci gaba da daukar matakan kariya.