Labarai
Gwamnatin Kaduna ta garkame gidajen saida abinci kan take dokar Corona
Ma’aikatar dake kula da harkokin kasuwanci,kirkire-kirkire da fasaha ta jihar Kaduna ta garkame gidajen saida abinci da kayan kwalama da kuma na barasa kuda 6 saboda take dokokin da aka shinfida don kare kai daga kamuwa daga cutar Korona.
An dai rufe gidajen saida abincin da kayan kwalam ne ya yin da ma’aikatar ke zagayen gani da idu don tabbatar ana amfani da dokokin da aka shinfida kan Corona wajen amfani da su a wuraren da ya dace don kare kai daga kamuwa da cutar COVID-19.
Kamfanin dilancin labaru na kasa ya rawaito cewa tawagar kwamishinan ta kai ziyarar ba zata ne Otel-Otel da gidanjen abinci da shaguna saida kayan kwalama na jihar ta Kaduna
Kwamishinan kasuwanci da fasaha na jihar Kaduna Sama’ila Idris-Nyam ne y sanar da hakan cewa, ayarin ma’aikatar ta ziyarci wuraren kasuwanci goma sha shida ya yin da ta kama 6 daga ciki da laifi.
You must be logged in to post a comment Login