Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano na shirin ba da damar fara harkokin karatu a Kwalejin Fasaha ta Gaya

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyar fara harkokin karatu a Kwalejin Fasaha ta Gaya Polytechnic nan ba da jimawa ba, yayin da ake ci gaba da aikin kafa makarantar.

 

Mai Taimaka wa Shugaban Kwamitin Aiwatar da Aikin makarantar Suhailu Tijjani Khalil, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Sanarwar ta ce, Shugaban Kwamitin, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, tare da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Ali Haruna Makoda, da Sakataren Kwamitin, Shehu Sani Shehu, sun gana da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda suka gabatar masa da rahoton ci gaban aikin.

 

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya gabatar da bayanai kan ayyukan da kwamitin ya gudanar, ci gaban da aka samu, ƙalubalen da aka fuskanta da matakan da ake ɗauka domin ci gaba da aikin.

 

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki domin kammala sauran sassan aikin, da nufin fara harkokin karatu a makarantar cikin zangon da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!