Labarai
Sokoto: Yan Sanda sun hallaka ƴan bindiga biyu tare da ƙwato bindigu kirar AK 47

Rundunar ’Yan Sandan jihar Sokoto ta ce, jami’anta sun hallaka ‘ƴan bindiga biyu tare da ƙwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu daga wajensu bayan daƙile harin da suka yi yunƙurin kaiwa ƙauyen Dankadu da ke Ƙaramar Hukumar Illela.
Hakan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar a baya baya nan.
Sanarwar ta kara dacewa lamarin ya faru bayan samun kiran gaggawa cewa wasu ƴan bindiga sun fito daga dajin Tsauna domin kai hari ƙauyen Dankadu.
Rundunar ta ce, jami’an tsaro sun yi musayar wuta da ƴan bindigar, inda suka hallaka biyu daga cikinsu tare da ƙwato bindigun AK 47 guda biyu, da harsasai 54.
You must be logged in to post a comment Login