Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano na shirin dasa bishiyoyi guda 10,000

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da fara karɓar buƙatun neman tsirran bishiyoyi a ƙarƙashin shirin dasa bishiyoyi miliyan 10, wanda ke da nufin yaƙi da hamada, farfaɗo da muhallin da ya lalace, da kuma rage illolin sauyin yanayi.

Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce ƙungiyoyin ci gaban al’umma, ƙungiyoyin sa-kai, ƙungiyoyin matasa, makarantu da cibiyoyin addini na iya neman tsirran domin dasawa a yankunansu.

Ya ce shirin na ci gaba ne da yunƙurin gwamnati na kare muhalli, yana kuma daga cikin manyan tsare-tsaren jihar na tinkarar sauyin yanayi da farfaɗo da muhallin da ya lalace.

A cewarsa, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bai wa ma’aikatar cikakken goyon baya domin aiwatar da shirye-shiryen da za su ƙara yawan bishiyoyi a fadin jihar.

Kwamishinan ya buƙaci ƙungiyoyin da ke da sha’awar shiga shirin su cike fom ɗin neman tsirran ta shafin da Gwamnatin ta samar

Dakta Dahiru Muhammad Hashim ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su rungumi wannan shiri a matsayin gudummawa wajen kare muhalli, yana mai cewa haɗin kan al’umma ne zai tabbatar da nasarar shirin dasa bishiyoyi miliyan 10 domin amfanin wannan ƙarni da waɗanda za su zo nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!