Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta karbi rahoton kwamitinta kan barkewar annobar tsutsar Tumatur

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karbi rahoton kwamitin Noma da Albarkatun kasa kan barkewar annobar tsutsar dake lalata tumatur ta Tuta Absaluta.

Shugaban Kwamitin Noma da Albarkatun Ƙasa na Majalisar, Alhaji Ahmed Ibrahim mai wakiltar Karaye, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton kwamitin a zaman majalisar.

Ya ce an bai wa kwamitin aikin binciken matsalar ne bayan wani ƙudiri na gaggawa da ɗan majalisar Bagwai/Shanono, Ali Lawan Kiyawa, ya gabatar kan yadda kwaron ke yaɗuwa a mazabarsa.

Rahoton ya nuna cewa kwaron ya bazu zuwa yankunan da suka haɗa da Bagwai da Shanono da Rogo sai Tofa da Bunkure da kuma Kura.

Ragowar sun hadar da Garun Malam da Rano da Kibiya da wasu sassan Tudun Wada da Dawakin Kudu.

Ahmed Ibrahim ya bayyana cewa kwaron na lalata tumatir tun daga matakin tsiro har zuwa girbi, inda yake lalata ganye, reshe, furanni da kuma ‘ya’yan tumatir, lamarin da ke haddasa asarar amfanin gona mai yawa idan ba a dakile shi ba.

Ya ƙara da cewa barkewar kwaron na iya jawo ƙarancin tumatir tare da tashin farashinsa a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Kwamitin ya buƙaci gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar kwaron, tare da tallafa wa Hukumar Bunƙasa Noma da Raya Karkara ta Kano da magungunan kashe ƙwari.

Haka kuma kwamitin ya ba da shawarar tura jami’an wayar da kan manoma zuwa yankunan da abin ya shafa, domin wayar musu da kai kan hanyoyin zamani na magance ƙwari, hana sayar da magungunan gona marasa inganci, da kuma tallafa wa manoman da suka yi asara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!