Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta dakatar da sare bishiyoyi a harabar gidan talabijin na jihar ARTV

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin dakatar da sare bishiyoyi ba tare da ka’ida ba a harabar gidan talabijin na jihar, Abubakar Rimi Television (ARTV), bayan wani bidiyo da ya karade  kafafen sada zumunta yana nuna yadda ake sare bishiyoyin.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayar da umarnin yayin wata ziyara ta bazata da ya kai tashar a ranar Asabar.

Ya ce sare bishiyoyin ya saɓa wa manufofin gwamnatin jihar na kare muhalli da yaƙi da sauyin yanayi, tare da gargadin cewa daga yanzu ba za a sare kowace bishiya a tashar ba sai an samu amincewar hukumomin da abin ya shafa.

Waiya ya kuma nuna damuwa kan yadda tashar ke gudanar da ayyukanta, yana mai cewa shirye-shiryenta da labaranta ba sa gamsar da masu kallo saboda rashin sabunta abubuwa da kuma ƙarancin ingancin labarai.

Ya bayyana cewa zai miƙa rahoto na musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin neman tallafi na musamman don inganta tashar da kuma mayar da ita ta zamani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!