Labarai
Gwamnatin Kano ta bada Umarnin a kama duk wanda yaki karbar tsahon kudi yayin cinikayya
Gwamnatin Kano ta ce zata rufe wurin sana’ar duk wanda ya ƙi karɓar tsohon kuɗi a hannun jama’a.
Shugaban Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA Baffa Babba Dan’agundi ne ya bayyana haka a yau.
Baffa Babba ‘Dan’agundi ya ce, Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayar da umurnin rufe duk wani gurin kasuwance a faɗin jihar nan da yaƙi karbar tsofaffin kuɗin.
Baffa Babba ya ce ”an ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-korafen jama’a da ya yi yawa na ƙin karɓar tsofaffin kuɗin a hannun jama’a, musamman a wasu daga cikin gidajen mai da Asibitoci da wajen saye da sayarwa na faɗin jihar nan.”
Hakan ya biyo bayan umarnin da babban bankin ƙasa CBN ya bayar na ci gaba da karbar tsofaffin kuɗin.
Tuni dai Gwamnan ya bayar da umurni ga Kwamitin Kar-ta-kwana mai kula da gidaje Mai su fita su tabbatar ana karɓar tsofaffin kuɗin.
Ya bayyana cewa duk wanda yaƙi bin umarnin ya saɓa da dokar Hukumar kula da Haƙƙin mai saye da sayarwa ta Consumer Protection Council, sashe na 10 ƙaramin sashi na 1(b) da kuma sashe na 10 ƙaramin sashi na 2 na dokar Hukumar
Ya ƙara da cewa ”duk wanda aka kama za a rufe wajen kasuwancinsa tare da gurfanar da shi a gaban Shari’a domin daukar mataki na gaba”.
Labari: Abba Isa
You must be logged in to post a comment Login