Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano ta fara bincike Kan sabuwar cutar da ta bulla a Bebeji
Gwamnatin jihar Kano tace ta fara gudanar da wani bincike akan zargin bullar wata cuta da take sawa wadanda suka kamu da ita Ciwon Kafa a garin Gargai dake karamar hukumar Bebeji domin dakile cigaba da yaduwarta.
Babban jami’i mai kula da sashen cututtuka masu yaduwa da bada rahotanni a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Dakta Sulaiman Ilyasu ne ya bayyana hakan, lokacin daya jagoranci tawagar likitoci zuwa garin na Gargai domin yin gwaje-gwaje don gano nau’in cutar da take damun al’ummar garin.
Dakta Sulaiman Ilyasu ya kara da cewa ‘ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta samu rahotan bullar cutar ne daga wajen dan majalisar Jiha mai wakiltar karamar hukumar Bebeji a zauren majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Ali Muhammad Tiga, inda suka gaggauta zuwa inda lamarin ya faru domin kai musu agaji.
A nasa bangaren dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Bebeji Ali Muhammad Tiga, yace ‘bayan ya samun rahotan bullar cutar ne ya garzaya ga kwamishinan lafiya na jihar Kano wanda a nan take ne ya bada umarnin tura tawagar likitoci domin a binciki lamarin.
Yanzu haka dai sama da mutane ashirin da hudu ne suka kamu da cutar, kuma kawo yanzu likitocin basu kai ga gano nau’in cutar ba domin daukar mataki na gaba har sai sun kammala bincike akai.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin kudu
You must be logged in to post a comment Login