Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta fara rangadin kananan Matatun Ruwa domin farfaɗo da su

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta fara rangadin duba ƙananan matatun ruwa da ke samar da ruwan sha ga al’ummomin karkara, a wani ɓangare na shirin farfaɗo da cibiyoyin samar da ruwa a faɗin jihar.

Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M. Hashim, ya ce an gudanar da rangadin ne tare da Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Masarautu, na Ma’aikatar Wuta da Tsaftataccen Makamashi, da kuma na Ma’aikatar Raya Karkara da Ci gaban Al’umma.

A cewarsa, sun ziyarci matatar ruwan Kusalla da ke samar da ruwa ga ƙananan hukumomin Karaye, Kiru da Gwarzo, da matatar ruwan Pada mai samar da ruwa ga Gwarzo, da matatar ruwan Magaga mai samar da ruwa ga Gwarzo da Kabo, sannan da matatar ruwan Guzuguzu mai samar da ruwa ga Kabo da Rimin Gado.

Ya bayyana cewa an tantance matsalolin da kowace matata ke fuskanta tare da tsara hanyoyin gyara da sabunta su, domin gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf don amincewa da aiwatar da aikin.

Dakta Dahir Hashim ya tabbatar wa al’ummar jihar, musamman mazauna Karaye, Kiru, Gwarzo, Kabo da Rimin Gado, cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen dawo da cikakken aikin waɗannan matatun ruwa domin samar da wadataccen ruwan sha ga al’ummomin yankunan da abin ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!