Labarai
NEC ta amince da ware fiye da biliyan 83 don rage illolin ambaliya

Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya NEC, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ta amince da ware Naira biliyan 83 da miliyan 200 domin aiwatar da shirye-shiryen rage illolin ambaliya da sauran bala’o’in da sauyin yanayi ke haddasawa a sassan ƙasar nan.
Amincewar ta biyo bayan gabatarwar Ministar Jiha mai kula da Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Doris Uzoka-Anite, wadda ta yi bayani kan muhimmancin ɗaukar matakan rigakafi domin rage asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon ambaliyar ruwa da ake fuskanta a duk lokacin damina.
Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen ƙarfafa shirye-shiryen gaggawa, tallafawa al’ummomin da ke cikin haɗari, da kuma bunƙasa hanyoyin kare rayuka da dukiyoyi daga illolin sauyin yanayi.
Hakazalika, NEC ta buƙaci gwamnatocin jihohi da su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen kawar da matsalolin da ke hana kayayyakin amfanin gona na Najeriya samun damar shiga kasuwannin ƙasa da ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login