Labarai
Dakarun sojin kasar nan sun hallaka yan ta’adda 60

Rundunar Sojin kasar nan, ta ce dakarunta sun hallaka ’yan ta’adda sittin da biyar tare da kubutar da mutane talatin da hudu da aka yi garkuwa da su, yayin wasu ayyukan da suka gudanar a sassan kasar cikin makon da ya gabata.
Daraktan yada labaran ayyukan tsaro na rundunar, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai.
Ya ce ayyukan sun gudana ne daga ranar 7 zuwa 13 ga watan Agustan 2026, inda dakarun suka ci gaba da kai farmaki kan maboyar ’yan ta’adda da kuma kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da ayyukan soji domin dakile ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da ke barazana ga tsaron al’umma.
You must be logged in to post a comment Login